1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a jaridun Jamus

Usman Shehu Usman RGB
July 16, 2021

Rikicin kasashen Habasha dana Afirka ta Kudu sun dauki hankulan jaridun Jamus a yayin da ake kara kira kan tallafawa kasashen nahiyar Afirka da riga-kafin cutar corona.

https://p.dw.com/p/3wa7q
Äthiopien Konflikt zwischen Konso & Ale
Rayuka sun salwanta a rikicin kasar HabashaHoto: Ale Communication Office

Habasha ta kara tsunduma cikin yaki a jihar Tigray inda yankin gaba daya rikici ya mamaye shi. Wannan shi ne sharhin jarida der Freitag. Jaridar ta ci gaba da cewa a wannan yakin, sojojin kasashen waje kamar Sudan da Eriteriya duk sun tsoma hannuwansu cikin rikicin. Mutumin da a shekarar 2019 ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, amma ya kasance jagoran yaki. A cewar jaridar da farkon zuwansa kan mulki a shekarar 2018, Abiy Ahmed ya zama babban misali, inda ya zo da kyakyawan shirin kawo sauyi, kana ya yi ta sakin fursunonin siyasa daga gidan yari, wanda ya sa duniya nan take ta yi maraba da shi, to amma abubuwa suka yi ta canzawa cikin sauri.

Südafrika | Ausschreitungen in Durban
Afirka ta Kudu na fama da rikiciHoto: AFP/Getty Images

Kwatsam Afirka ta Kudu ta fada cikin rudani. A sharhinta jaridar die Tageszeitung, ta ce akalla mutane 72 sun mutu a tarzomar da ta barke. Musabbabin tarzomar, ya samo asali ne daga magoya bayan tsohon shugaban kasa Jacob Zuma, wanda suka fara zanga-zangar adawa da hukunci daure shi a gidan yari. Amma daga bisani, boren ya rikede zuwa fushin da tsadar rayuwa wanda talakawan kasar suka dade suna fama da shi. Matasan dai sun yi ta balle shaguna, suna kwasar ganima suna kone-konen dukiyoyi, 'yan sanda sun mayar da martani mai tsauri wanda har ta kai ga mutuwa. Jaridar ta ce boren ba komai bane illa nuna yadda tsaffin masu fafitika a gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata, sai kuma suka hade da ma goya bayan Jacob Zuma.
Faransa na kokarin tsame kanta daga yankin Sahel wannan shi ne labarin jaridar Neue Zürcher Zeitung. Kawo karshen zaman sojojinsu a sansanin Barkhane tun a watan da ya gabata, Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da hakan. Abin da hakan yake nufi babu wanda ya sani, illah kawai ya yi ganawarsa da shugabannin kasashen Mali, Nijar, Burkina Faso da Chadi da kuma Mauritaniya. Faransa na son rage sojojinta a rundunar G5 Sahel su kasance 5100 kafin karshen wannan shekarar, kana izuwa shekaru biyu nan gaba sojojin za su rage ya saura 2500 kacal. Hakan dai yana nufin janye dakarun Faransa daga kasar Mali, wanda kawo yanzu Faransar ke da sansanoni har shida a cikin kasar wanda sansanin yankin Gao shi ne mafi girma. Tun daga watan gobe za a janye dakarun Faransa daga sansanoni uku da suka hada da Kidal, Tessalit da kuma Timbuktu. 
Ita kuwa jaridar Die Welt ta yi tsokaci ne kan allurar riga-kafin corona a Afirka, jaridar ta duba jawabai da gwamnatin Jamus ke yi a yunkurin neman kasashen duniya su dau matakan gaggawa wajen samar da allurar riga kafin corona ga kasashe matalauta. Jaridar ta ruwaito ministan raya kasashen Jamus Gerd Müller na mai cewa, kamata yayi sauran kasashe da ke da karfin tattalin arziki su yi koyi da Jamus,  don tsamo kasashen Afirka cikin matsalolin da suka fada musamman bayan bullar corona. Don haka Müller ya ce nauyi ne kan kasashen masu karfi, kan su dau matakan tallafawa matalauta. Minista raya kasashen na Jamus ya bada hujjar cewa kusan waji bi ne fa ga kasashen kamar su Jamus kai tallafi a Afirka, domin idan har kasashen da ke da wadatattun alluran riga-kafi, suka ki yin hakan, to kuwa akwai hatsarin alluran da yanzu suka tara za a kai ga lokacin aikinsu ya kare ba a yi aiki da su, wanda kuma sun zama shara kenanan yayin da a wasu kasashen ake matukar bukatarsu.

Elfenbeinküste | Coronakrise: Impfstart
Afirka na fama da karancin riga-kafin coronaHoto: Cyrille Bah/AA/picture alliance
Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Rundunar sojin BarkhaneHoto: AP Photo/picture alliance