1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Usman Shehu Usman RGB
November 18, 2022

Farmakin 'yan tawayen M23 a Kwango da kokarin kau da hukuncin kisa a kasashen Afirka, na daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4JlNB
Rikici ya daidaita jama'a a GomaHoto: GUERCHOM NDEBO AFP via Getty Images

Jaridar Die Tageszeitung ta ce, Kungiyar 'yan tawayen M23 na ci gaba da kai farmaki kan birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango. Tsoro ya cika 'yan gudun hijirar da yaki ya daidaita. Jaridar ta ci gaba da cewa harguwar Goma, shelanta yaki kan 'yan tawayen M23 Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, sojojin gwamnatin kasar sun riga sun fice daga birnin. Babban birnin lardin Kivu ta arewa da ke gabashin Kwango zai fada hannun 'yan tawaye ba tare da fada ba. Kusan shekaru goma bayan da 'yan M23 suka yi wa Goma mamayar ba-zata, wasan kwaikwayo yana sake maimaita kansa. Firgici ya barke a birnin miliyoyin da ke gabar tafkin Kivu da kuma sansanonin 'yan gudun hijira da ke kewaye.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung, ta fara sharhinta kan Afirka da aza ayar tambaya kamar haka. Ta ce me za a yi da ajiyar iskar gas? A Afirka, kishirwar makamashi na Turai na cin karo da kokarin inganta yanayin kare mahalli. Shekara guda da ta wuce, sama da kasashe 20 sun yi alkawarin dakatar da bayar da tallafin ayyukan kasashen waje da hako ma'adinai masu haddasa gurbata mahalli. Amurka ta shiga sahu, amma ita ma Italiya da Denmark ba a barsu a baya ba. Wannan sanarwar a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a Glasgow, ya gamu da amincewa daga ko'ina a sassan duniya. A karshe, magana ta zo kusa da cewa yawancin adadin albarkatun mai, ya kamata su kasance a karkashin kasa inda har yanzu akwai damar cimma burin yanayi na duniya.

Aktivist Eric Njuguna auf der Klimakonferenz COP26
Dan rajin kare muhalli Eric Njuguna Hoto: Eric Njuguna

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung, a wani labari ta duba ne yadda nahiyar Afirka ke zama fagen yaki na neman baza komar manyan kasashen duniya. Afirka na kara habbaka zuwa yanki na siyasa da ke da tasiri da kuma ke hade da rikici. Jaridar ta ce, dole ne kasashen yamma su daidaita da kyau a bisa gasarsu da Chaina da Rasha a Afirka. Yanzu manyan kasashen duniya Chaina da Amirka, Tarayyar Turai da Rasha sun kara zage damtse wajen kafa madafun iko a kasashen Afirka. Abin da ke faruwa a yanzu game da wannan yunkurin da ake yi shi ne, yakin da Rasha ke yi da Ukraine. Kasashe 54 na Afirka sun kasance kusan kashi daya bisa uku na kasashe membobin Majalisar Dinkin Duniya, don haka suna da tasiri sosai kan kuri'u da nadi a kungiyoyin duniya. Baya ga ma'aunin diflomasiyya na Afirka, musamman ma dacewarta ta fannin dabarun kasa da kuma karfin tattalin arzikinta ne ke tabbatar da sabon sha'awar da aka samu na kulla alaka mafi kusa da Afirka.

Annalena Baerbock
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena BaerbockHoto: Christophe Gateau/dpa/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung kuwa, ta duba batun neman a soke hukuncin kisa a Nahiyar Afirka, tana mai cewa Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi kira ga sauran kasashe da su soke hukuncin kisa. Ana kashe mutane dubbai a kowace shekara a duniya. Har yanzu ana aiwatar da hukuncin kisa a fiye da kasashe 50 na duniya. Baerbock ta bude taron Majalisar Dinkin Duniya game da hukuncin kisa, a taron da ke gudana duk bayan shekaru uku a Berlin a ranar Talatar da ta gabata. Kungiyoyin farar hula ne suka shirya taron na yaki da amfani da hukuncin kisa.