1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal AMA
December 11, 2020

Zaben shugaban kasa a Ghana da rikicin siyasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma rikicin yankin Tigray a Habasha sun mamaye jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3ma85
Afrika Ghana Präsidentschaftswahlen
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: AP Photo/picture alliance

Jaridar Die Tageszeitung ta ce shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya lashe zaben shugaban kasa sai dai akwai rashin tabbas kan daidaito rinjayd a sabuwar majalisar dokoki, abin da zai kawo cikas wajen yin aiki tare. A zaben na ranar Litinin shugaban mai shekaru 76 na jam'iyyar NPP ya samu kimanin kashi 51 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada yayin da tsohon shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar adawa ta NDC, John Mahama wanda ya kuma ya shugabanci kasar daga 2012 zuwa 2016, ya samu kimanin kashi 48 cikin 100, amma 'yan takaran sauran jam'iyyu 10 ciki har da uwargidan tsohon shugaba marigayi Jerry John Rwalings wato Nana Konadu Agyeman-Rawlings ba su kai labari ba. An samu karuwar yawan masu kada kuri'a da suka kai miliyan 12.8 idan aka kwatanta da miliyan 10.8 a shekarar 2012. Hakazalika zaben da aka hada har da na 'yan majalisa ya tafi salin alim, in ban da wasu rigmu da ba su taka kara suka karya ba. NPP ta rasa kujeru 31 na majalisa yayin da NDC ta sami karin kujeru 30, yanzu kusan sun yi kunnen doki a yawan kujeru a majsalir mai kujeru 275, abin da ko shakka babu zai kawo cikas wajen aiwatar da aikin shugaban saboda rashin gagarumin rinjaye.

A Tigray jama'a na cikin dimuwa

Karin Bayani : Sharhi kan zaben Ghana na 2020

Äthiopier Flüchten vor Kämpfen in Tigray in den Sudan
Yan gudun hijirar yankin Tigray na HabashaHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce a wannan mako ta leka yankin Tigray mai fama da rikici a kasar Habasha. Ta ce mutane da yawa na jiran samun taimako amma har yanzu shiru, hakan ya zo ne bayan da rundunar sojojin Habasha ta yi shailar samun nasara a rikicinsu da 'yan gwagwarmayar kungiyar kwatar 'yancin Tigray. A ranar 28 ga watan Nuwamba Firaminista Abiy Ahmed ya ce an yi nasarar murkushe abin da ya kira bori a yankin na arewacin kasar. Kuma a ranar 2 ga watan nan na Disamba Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita da gwamnatin Habasha sun cimma yarjejeniya da ta ba da tabbacin kai kayan jin kai kamar abinci da magunguna ba tare da  cikas ba. Sai dai mako guda bayan wannan yarjejeniya hanyoyi da tanade-tanaden kai kayan agaji yankin na Tigray ba samu ba, sai a ranar Lahadi wasu bayanai suka ce wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta kama hanyar zuwa yankin, amma sojoji sun hana su zuwa sansanin 'yan gudun hijirar Eiritiriya da ke Shimelba. Gwamnatin Habasha ta ce tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya ta je wani yanki da ba a nan ya kamata ta tafi ba. Har wannan mako dai aikin kai agaji a yankin na Tigary na tafiyar hawainiya.

Karin Bayani : Gwamnatin Habasha ta karbe iko da Tigray

Shugaba Tshisekedi ya raba gari da Kabila

Bildkombo I Félix Tshisekedi und  Joseph Kabila
Shugaba Félix Tshisekedi da Joseph Kabila

Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya sanar da kafa abin da ya kira sabon harsashi na kasa, inda ya ce zai rushe kawancen da suka kulla da tsohon shugaban kasa Joseph Kabila, inji jaridar Die Tageszeitung. Jaridar ta ce wannan mataki na barazanar janyo rikici a kasar. Shugaban ya ce ya nada wani wakili da zai gabatar da wani tsari kan sabon rinjaye a majalisar dokoki, idan hakan ba ta samu ba zai rusa majalisa ya kuma kira sabon zabe. Ya ce mafi yawan al'ummar kasar za su yi watsi da kawance tsakanin jam'iyyarsa da ta Kabila, domin kawancen ya gaza biyan bukatun al'ummar kasar. Sai dai ganin yadda Kabila ke da gagarumin goyon baya na hukumomin tsaron kasa, wannan mataki na Shugaba Tshisekedi ka iya jefa kasar cikin rudani. Karin Bayani: Sharhin Jaridun Jamus 04.12.2020

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani