Afirka a jaridun Jamus 02.10.2020 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a jaridun Jamus 02.10.2020

Zargin yin lalata da cin zarafi a lokacin barkewar annobar Ebola a Janhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da yunkurin kamfanonin hakan zinariya na inganta rayuwar mazauna yankunan da suke aikin sun ja hankalin jaridun Jamus.

Bari mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda a wannan mako ta yi sharhi kan aikin hakan gwal ko zinari tana mai cewa kamfanonin hakan zinariya sun lashi takobin yin aiki don inganta rayuwar mazauna yankunan da ke da wannan arziki na karkashin kasa na nahiyar Afirka. Jaridar ta ce a karon farko Majalisar Gwal ta Duniya ta bayyana aikin mahaka da ke da burin ba da gudunmawa don cimma muradun ci-gaba masu dorewa na Majalisar Dinkin Duniya kafin shekara ta 2030. Wuraren hakan zinariya dai na nesa da birane, wurare ne kuma da babu ababan more rayuwa. Kamfanonin hakan gwal na samar da aikin yi suna kuma tallafa wa al'ummomin yankuna, sai dai a kasashe masu arzikin zinariya a Afirka irin su Afirka ta Kudu da Ghana, sau da yawa ana aikin ba tare da la'akari da illar da ake wa muhalli ba, lamarin da ke jefa rayuwar al'umma cikin garari, domin suna rasa gonakinsu da sauran wuraren sana'o'in da suka gada daga kaka da kakanni. Fata a nan shi ne Majalisar Gwal ta Duniya ta cika alkawarin da ta dauka na inganta rayuwar al'ummomin yankunan da ake hako arzikin na karkashin kasa a ciki.

Zargin likitoci da cin zarafin mata a Kwango

Kongo Mbandaka Ebola

Jami'an kiwon lafiya masu yaki da Ebola

Zargin yin lalata da cin zarafi lokacin barkewar annobar Ebola a baya bayan nan a Janhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya ta da hankalin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce a ranar Talata da ta gabata shugaban WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ba da sanarwar cewa za a gudanar da gagarumin bincike na zargin da ake wa wasu likitoci da ma'aikatan wasu kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya za kuma a dauki matakan da suka dace a kan wadanda aka samu da laifi. Rahotannin dai sun ce fiye da mata 50 ne a Kwango ke zargin ma'aikatan WHO da wasu kungiyoyi na duniya da yin lalata da su don su ba su aiki. Lamarin ya faru ne tsakanin watan Agustan 2018 zuwa wata Mayu wannan shekara ta 2020, lokacin da cutar Ebola ta sake barkewa a gabashin Kwango. Wasu matan ma na zargin wasu jami'an ma'aikatar kiwon lafiya ta Kwango da hannu a cikin aika-aikar. Jaridar ta ce wannan badakala na zama babban naushi ga hukumar WHO, da ke shan suka daga hukumomin Amirka saboda zarginta da yi wa kasar Chaina sassauci a kan cutar corona.

Zambiya na dab da rugujewa

Afrika Sambia Coronavirus Vorkehrungen

Dan kasar Zambiya sanye takunkumi

 Kasar Zambiya na dab da talaucewa, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Ta ce Zambiya ka iya zama kasar Afirka ta farko da gwamnatinta za ta kasa biyan kudaden ruwa na bashi da ta ciyo, saboda cutar corona. Wasu kasashen Afirka ka iya bin sahunta. Jaridar ta ce a shekarar 2012 Zambiya ta ciri tuta a tsakanin kasashen Afirka a bangaren tattalin arziki, abin da ya sa wasu masana suka ce tana iya zama abar koyi ga sauran kasashen Afirka. Amma yau shekaru takwas baya, kasar ta fada cikin matsalolin kudi sakamakon annobar corona da ta gurgunta harkokin kasuwanci da na ciniki tsakanin kasar da kasashen duniya, abin kuma da ka iya bazuwa sauran kasashen yankin irin su Angola, Jamhuriyar Kwango, Gabon da kuma Mozambik.

Sauti da bidiyo akan labarin