Afiika ta dauki aniyar saukaka harkar sufurin sama a nahiyar | Labarai | DW | 29.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afiika ta dauki aniyar saukaka harkar sufurin sama a nahiyar

A karshen taron kolinsu a birnin Addis Ababa, shugabannin Afirka sun kuduri aniyar saukaka harkar sufurin sama tare da kaddamar da kasuwanci maras shinge.

An kammala taron shugabannin kasashen Afirka na kungiyar AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda taron ya amince da wasu matakai kan inganta sufurin jiragen sama a nahiyar baki daya gami da daukar matakin inganta kasuwanci da hada-hadar mutane.

Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce yana goyon bayan duk matakin da kasashen Afirka suka dauka game da magance rikice-rikice da ake samu a nahiyar ya kuma kara da cewa:

"Mun yi imani da 'yan Afirka su samar wa kansu mafita game da rikice-rikicen da ake samu a nahiyar, kamar Majalisar Dinkin Duniya na tare da kungiyar gabashin Afirka da ta tarayyar Afirka game da magance rikicin Sudan ta Kudu. A iya sani na abu ne mai wahalar gaske matakan tsaro su dauki wani mataki ba tare da hadin kai dukkan bangarori ba."

Fiye da shugabannin kasashe da gwamnatoci 40 ne suka halarci taron a birnin Addis Ababa, taron da halin yanzu akwai kyakykyawan zaton zai kawo karshen kashe makuden kudade da al'ummar nahiyar Afrika suka jima suna yi don yin tafiye-tafiye ta jiragen sama.