1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum 15 sun mutu a yunkurin neman visa

Ramatu Garba Baba
October 21, 2020

Mutum kimanin 15 ne suka mutu a yayin wani cunkoson jama'ar da ke kokarin neman takardar visa don samun izinin shiga kasar Pakistan da ke makwabtaka da kasar ta Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3kDVH
Afghanistan Toten nach einem Explosion in Provinz Wardak
Hoto: Ashaq Akrami/DW

Yan kasar Afghanistan kimanin goma sha biyar ne suka rasa rayukansu a sanadiyar cunkoson da aka samu a kusa da ofishin jakadancin kasar Pakistan da ke kasar, goma daga cikin mamatan mata ne sauran kuma tsofaffi.

Rahotanni sun ce, lamarin ya auku ne a yayin da mutum sama da dubu uku, ke rige-rigen bin layi don samun takardar visar shiga kasar Pakistan. Kawo yanzu dai babu karin haske daga jami'an ofishin jakadancin na Pakistan a game da lamarin.