Afghanistan: An dakatar da bude wuta na mako guda | Labarai | DW | 21.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afghanistan: An dakatar da bude wuta na mako guda

A wannan Juma'ar Amurka da wakilan Taliban da rundunar gwamnatin Afghanistan suka cimma matsaya kan dakatar da kai hare-hare kan juna a kasar ta Afghanistan na tsawon mako guda.

A wannan Juma'ar, Amurka da bangaren Taliban da rundunar gwamnatin Afghanistan suka cimma matsaya kan dakatar da kai hare-hare kan juna a kasar Afghanistan. Mako guda ake son ganin an bi don mutunta wannan doka, wanda idan an yi nasara, sai a dora da yarjejeniyar da aka shata a can baya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da ya fidda wannan sanarwar a shafinsa na tweeter, bai yi karin bayani kan manufar son ganin an rage hare-haren ba, sai dai ya ce manuniya ce a game da inda aka dosa a kokarin samar da zaman lafiya a kasar da aka kwashi sama da shekaru goma sha takwas ana fama da rikici.

A ranar ashirin da tara na wannan watan Febrairun da muke ciki, bangarorin za su rattaba hannu a hukumance a kan yarjejeniyar a birnin Doha, tuni Mista Pompeo ya shawarci bangaren Afghanistan da su yi amfani da wannan damar don ganin an cimma zaman lafiya na din-din.