1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFCON: Senegal za ta fuskanci Maroko a wasan karshe

January 15, 2026

Duk da rawar gani da ta kai Najeriya matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin Afirka, Super Eagles sha kaye a hannun Maroko, a wasan da aka kare da bugun fenarati a dare jiya.

https://p.dw.com/p/56qEf
Yadda 'yan Maroko ke murnin nasara kan Najeriya bayan wasa
Yadda 'yan Maroko ke murnin nasara kan Najeriya bayan wasaHoto: Hicham Driouich/DW

Senegal da mai masauki Morocco sun tsallake zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afirka (AFCON), bayan da suka yi nasara a wasanninsu na zagayen dab da na karshe a daren jiya.

Zakunan Teranga na Senegal sun doke Masar da ci daya da nema, inda Sadio Mané ya zura kwallo daya tilo a minti na 78.

A daya wasan kuma, Najeriya ta fice bayan da Morocco mai masauki ta doke ta a bugun fenarati da ci 4–2, bayan kammala cikakken lokaci na wasan da ma karin mintuna 30 babu wanda ya zura kwallo.

A ranar Asabar, Masar da Najeriya za su kara a birnin Casablanca domin neman matsayi na uku.

Sai kuma ranar Lahadi, Senegal da Morocco za su fafata a wasan karshe a birnin Rabat domin sanin wadda za ta lashe kofin na bana.