Aecio Neves ya samu goyon bayan Marina Silva | Labarai | DW | 12.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aecio Neves ya samu goyon bayan Marina Silva

'Yar takarar da tazo ta uku a zagaye na farko na zaben shugaban kasar Brazil ta amince ta hada karfi da Aecio Neves domin kalubanantar Dilma Rousseff a zagaye na biyu.

Marina Silva ta ce ganin irin-irin burin da Neves ya sa a gaba, to dole ne ta kada masa kuri'ar ta, kuma tana mai goyon bayan takararsa. Ta yi wadannan kalammai ne yayin wani zaman taro da suka gudanar a birnin Sao Paulo. Sakamakon zagayen farko na zaben dai, ya baiwa Shugaba Dilma Rousseff kashi 41.6 cikin 100, yayin da Aecio Neves yazo na biyu da kashi 33.6 cikin dari, inda Marina Silva da tazo ta uku ta samu kashi 21 cikin 100 wanda ake ganin idan magoya bayanta suka yi biyayya ga wannan umarni, to wanda ta dafawa ne zai ci zaben.