Addu′o′i dan samun zaman lafiya a jihar Borno | Siyasa | DW | 11.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Addu'o'i dan samun zaman lafiya a jihar Borno

Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya umurci al’ummar jihar ta yi azumi na tsawon kwanaki uku wanda za a kammala da addu’o’i na musamman ranar Juma’a domin samun kwanciyar hankali a wannan yankin.

Al'ummar jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Najeriya sun tashi da azumi yau tare da gudanar da addu'o'i na musamman don neman Allah ya kawo karshen tashe-tahsen hankulan da ake dangantawa da Boko Haram.

Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi shine ya umurci al'ummar jihar su fara azumi na tsawon kwanaki uku inda kuma za'a yi addu'o'i na musamman a ranar Juma'a domin neman mai kowa mai komai ya kawo karshen zubar da jinin bayain Allah da ake yi a wannan yankin.

A cewar Shehun Bornon matsalar tsaron ta wuce tunanin al'umma shi ya sa ya zama dole a koma ga Allah domin neman sauki. Al'ummomin jihar Borno musamman mazauna garin Maiduguri sun amsa kiran da tashi da azumi da kuma yawaita karatun Al'Qur'ani mai girma kamar yadda wasu mazauna birnin Maiduguri suka bayyana min.

Malaman addinin Maiduguri sun goyi bayan adduo'in

Malam Mai Dala'ilu Musa wani malamin addinin musulunci ne a Maiduguri ya tabbatar min da cewa jama'a da dama sun dauki azumin saboda yadda matsalar tsaron ke neman rutsawa da kowa.

Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi of Borno ACHTUNG QUALITÄT

Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi

"Wasu suna yi, wasu kuma ba sa yi amma a zahirin gaskiya wadanda suka dauki azumin sun fi yawa saboda kowa ya damu da abinda ke faruwa na kashe-kashen mutane a nan jihar Borno da sauran sassan kasar kuma suna jin labarin matsalar daga nesa yanzu ta fara isowa kusa da mutane, saboda musulunci ya tanadi in an samu masifa irin haka a ayi addu'o'Iimuna azumi tare da yin tawassuli da Manzon Allah, Allah Ya kawo mana zaman lafiya”

Mata ma ba a bar su a baya ba wajen amsa umurnin Shehun na Borno, Malama Zainab Muhammad wacce take da zama a garin Maiduguri ta bayyana min dalilin su na yin azumin a wannan lokaci.

“Domin abinda ake yi a garin mu da sauran yankuna makotanmu abin ya dame mu matuka muna fatan da wannan azumi da addu'o'i da zamu yi Allah ya kawo mana saukin wannan matsalar ta rashin tsaro. Mata da yawa sun dauki azumin domin zubar da jinin ‘yan uwa da ake yi ya dame mu, ba ma jin dadi har zukatan mu”

Ba kowa ne ya amsa wannan kiran ba

To sai dai akwai wasu da ba su dauki wannan azumi ba inda kowa ke bada dalilin sa, wanda kuma ya sha banban da na dan uwan sa, a yayin da wasu ke cewa rashin kwanciyar hankali wasu kuma na ba da dalilin rashin masu gidan rana. Amma ga Malam Sagiru Ahmadu halin Shugabannin ne ya hana shi daukar wannan azumi kamar yadda ya shaida min ta wayar tarho.

Bombenanschlag in Maiduguri Nigeria ARCHIVBILD 2012

Tsaro ya taɓarɓare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

“Abinda ya sa ban fara yin wannan azumi ba shi ne saboda wadannan shugabannin, abubuwa na faruwa ba su magana ba su damu da mu ba sai yanzu da suka ga wuri ya kure musu suke neman a yi azumi. Rashin adalcin da ake mana ya isa. Ko ba a ce mana mu yi azumi ba muna yi, kuma kullum a ckin addu'a muke”

Dakarun Najeriya sun fara yin galaba a dajin Sambisa

Mataki na yin azumi da addu'o'in na zuwa ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa ana gwabza fada a dajin Sambisa bayan da Sojojin Najeriya suka kutsa dajin wanda ake zargin akwai sansanonin kungiyar Jama'tu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko Haram a ciki.

Wannan ya sa mutane ke ganin yin addu'ar zai iya tasiri a samu bakin zaren warware wannan matsalar da hallaka dubban mutane tare da gurgunta tattalin arzikin kasa na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Shehun Bornon ya kuma nemi Kiristoci da yanzu haka suke yin nasu azumin suyi addu'o'i a majami'un su ranar lahadi inda ya bukaci sauran al'ummomi na kasar nan su ma su taya su yin azumin da addu'o'i don Allah ya kawo karshen zubar da jinin a jihar da Najeriya baki daya.

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Pinaɗo Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin