Adadin ′yan gudun hijira ya karu a duniya | Labarai | DW | 20.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adadin 'yan gudun hijira ya karu a duniya

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin 'yan gudun hijira ya kai miliyan 65, abinda ke nuna cewar yawan 'yan gudun hijira ya karu fiye da shekarun baya.

Wani rahoto da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato ta wallafa a wannan Litinin din albarkacin ranar 'yan gudun hijira ta duniya ya nunar da cewa adadin mutanen da suka bar muhallansu a dalilin yaki ko wata tsangwama a duniya a shekara ta 2015 ya kai adadin da ba a taba samu ba a tarihi inda ya kai miliyan 65 da dubu dari uku.

Hukumar ta ce tun soma yaki a Siriya a shekara ta 2011 adadin 'yan gudun hijirar na karuwa ne a ko wace shekara bayan kuwa sai da ya daina karuwa tsakanin shekara ta 1996 zuwa ta 2011. A takaice idan aka kwatanta da shekara ta 2014 to adadin 'yan gudun hijirar ya karu da kashi 9,7% a shekara ta 2015: