Adadin ′yan gudun hijira ya kai mataki kamar lokacin yakin duniya na biyu | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Adadin 'yan gudun hijira ya kai mataki kamar lokacin yakin duniya na biyu

Adadin 'yan gudun hijira ya haura fiye da kowane lokaci tun shekarun 1950 da aka fara kirga yawan 'yan gudun hijira

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira Antonio Guterres ya bayyana cewa rikice-rikice da ake fuskata a kasashen duniya, da gazwa da aka yi na samar da mafita sun haifar da 'yan gudun hijira kimanin milyan 60.

A cikin rahoton shekara-shekara da ya gabatar a birnin Geneva na kasar Switzerland jami'in ya ce an samu lamari kamar lokacin yakin duniya na biyu, inda a shekarar da ta gabata aka samu mutane milyan 59 da rabi a matsayin 'yan gudun hijira, wasu a cikin kasashensu yayin da wadanda suka tsallaka kan iyaka, kuma kasashen Siriya, da Somaliya, da kuma Afghanistan ke kan gaba wajen yawan 'yan gudun hijira a duniya.

Sannan ga 'yan gudun hijira da suka samun tsallaka tekun Bahar Rum kasashen Italiya da Girka, da Jamus da Sweden ke kan gaba a wurin da 'yan gudun hijira ke neman zama a Turai.