1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Rikicin Hamas da Isra'ila na kara ta'azzara

Abdoulaye Mamane Amadou
March 12, 2024

M'aikatar lafiya a yankin Gaza ta tabbatar da da mutuwar Falasdinawa dubu 31 da 184, tun bayan da dakarun Isra'ila suka soma kutse a yankin a kokrinsu na kakkabe mayakan Hamas.

https://p.dw.com/p/4dQup
Isra'ila na luguden wuta a Khan Yunis na kudancin Gaza
Isra'ila na luguden wuta a Khan Yunis na kudancin GazaHoto: Ismael Mohamad/UPI Photo/IMAGO

A cikin rahotonta na rana-rana da take fitarwa, ma'aikatar lafiyar yankin Falasdinu ta ce akwai wasu fiye da mutane dubu 72 da suka jikkata, watanni shida bayan da bangarorin biyu na Hamas da Isra'ila suka soma gwabza fada.

Rahoton ma'aikatar lafiya a Gaza ya ce ko a sa'o'i 24 da suka wuce, hare-haren dakarun Isra'ila sun kashe mutane 72 a yankin.

Wannan kuwa na zuwa a yayin da ministan harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari, ya ce kasar Qatar da kawayenta, sun kasa shawo kan bangarorin Isra'ila da na Hamas kan batun tsagaita wuta tare da sakin Isra'ilawan da ake garkuwa da su.