1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin Falasdinawa da suka halaka sun kai 58

Yusuf Bala Nayaya
May 15, 2018

Ma'aikatar lafiya a yankin Gaza ta bayyana cewa Falasdinawa 58 ne suka rasu ciki har da dan jariri da ya rasu sakamakon hayaki me sa hawaye da ya shaka baya ga 57 da suka rasu sanadin ruwan alburusan sojan Isra'ila.

https://p.dw.com/p/2xj9q
Israel Protesten in Gaza
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com/A. Amra

A cewar ma'aikatar lafiya a yankin Gaza shida daga cikin adadin dai kananan yara ne akwai kuma sama da 2,700 da suka samu raunika 1,360 cikin wannan adadi ta sanadin alburusan bindiga na gaske. Wannan dai na zuwa ne yayin da dubban Falasdinawa suka gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin don nuna adawa da shirin bude ofishin jakadancin Amirka a Birnin Kudus, matakin da ke shan suka tsakanin kasa da kasa, sai dai a bangaren Amirka ta ce rasa rayukan da aka samu sanadin kisan Falasdinawan alhaki ne da ya rataya a wuyan kungiyar Hamas ta Falasdinawa. A nata martanin kungiyar Amnesty International ta ce lokaci fa ya yi na dena yin Allah wadai da kasashe ke yi na jeka na yika kan wannan batu a dauki mataki kan Isra'ila kamar yadda Magdalena Mughrabi mataimakiyar darakta me kula da yankin Gabas ta Tsakiya a kungiyar ke bayyanawa.