Abuja: Ba Nakasasshe sai kasasshe | Himma dai Matasa | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Abuja: Ba Nakasasshe sai kasasshe

Wani nakasshe mai hataka da ke sana'ar gyara da kuma yin sabbin takalma a shagonsa da ke Abuja.Sabanin yadda masu tawayar halitta ke dogaro da yin bara.

A Najeriya ba kasafai ake samun nakasassu da kan rungumi sana'a har su dogara da kansu ba, musamman wadanda nakasar tasu ta kai ga tawaya ga kafafu ko hannuwansu. To sai dai ga Ibahim Salisu Gano ya cira tuta, inda yake kware a sana'ar gyara da ma kera sabbin takalma a Abuja.

Idan da hanya zata bi da kai ta gaban shagon Ibarahim Balarabe zaka dauka daya daga cikin irin nakasassun nan ne da ke jiran fara yi maka magiya don a basu sadaka. Amma ina ba haka lamarin yake ba, domin Ibarahim Balarabe shi ne ma Oga a shagonsa da ya ke gyaran takalma har ma da kera sabbi. Shin me ya dauki hankalinsa ya fara wannan sana'a maimakon bara da mafi yawan naksassu suka fi dogara da ita?

Demokratische Republik Kongo Stadt Bukavu Straße Straßenszene

"Na shiga wannan sana'a ner domin in taimaki kaina da ‘yan uwana, kuma a gaskliya ni bana sha'awar bara , domin ana saye a hanuna kuma ina taimakon kaina da ‘yan uwana".

Wani abnida ya dauki hankali shine yadda duk da hali na nakasa Ibrahim Gano ya samu kwarewar da yake kera sabbin takalama a shagonsa, inda ya yiwa masu kafafu da ke irin wannan sana'a zarra domin su da kan kwasi tsawon yini suna zagawa bas u kai wannan matsayi ba, shin ta wace hanya ya kai ga haka?

"Allah ya taimakemu a lokacin mulkin Kwankwaso an debe mu a tsarin na ba nakasasshe sai kasasshe, an debi mafi yawan nakasassu an kaimu Mariri kowa ya koyi sana'ar hannu. Duk da ya ke iyayena ba masu karfi ba ne ammna na yi kokari na samu jalli da nike wannan sana'a don in rufawa kaina asiri".

Ga masu sana'ar gyaran takalma da ba nakasassu ba na ganin wannan babban kalubale ne a garesu da ma sauran nakasassu kamar yadda Malam Abubakar Tanko mai gyaran takalma ya bayyana.

"Lallai hakika muna jin dadi in muka gansu saboda muma rashin zauna wurin daya nan shi yasa muke haka, don in muna zaune a wuri daya dole ne mu tanaji wadannan kayayyakin na gyaran takalmin, inji da sauran fata wanda zamu hada takalama".

Zuciyar Ibrahim Gano matashin da duk da nakasarsa ya kasance mai dogara da kansa na cike da burin a ganin nakasassu sun a Najeriya da ma Afirka sun kasance masu dogaro da kansu don an ce ba nakasasshe sai kasasshe.