Abdelaziz Djerad ya zama firaministan Aljeriya | Labarai | DW | 28.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abdelaziz Djerad ya zama firaministan Aljeriya

Shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya nada Abdelaziz Djerad a matsayin sabon firaministan kasar.

Sabon firiministan Djared mai shekaru 65 da haihuwa tsohon jami'in diflomasiyya ne wanda ke koyar da kimiyyar siyasa a jami'ar birnin Aljes, kuma ya taba zama ministan harkokin waje a tsohuwar gwamnatin Aljeriya da ta shude.