A yau Laraba Ne Shugaban Kasa Johannes Rau Ke Ban-Kwana | Siyasa | DW | 30.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

A yau Laraba Ne Shugaban Kasa Johannes Rau Ke Ban-Kwana

Bayan shugabanci na tsawon shekaru biyar, a yau laraba shugaban kasar Jamus Johannes Rau ke bankwana daga wannan mukami

Bikin ban-kwana da aka shirya wa shugaban kasa Johannes Rau

Bikin ban-kwana da aka shirya wa shugaban kasa Johannes Rau

Ba za a iya kimanta matsayin jami’in siyasa a lokacin da yake kan zamaninsa ba ta la’akari da ire-iren abubuwan dake faruwa yau da kullum da kuma gudun cusa wa jama’a wani ra’ayi a game da shi. A kuwa wannan marra da muke ciki ba zamu iya kimanta rawar da Johannes Rau ya taka a karagar shugabancin Jamus ba sai daga baya. Amma akalla muna iya cewar wanzar da manzancin da aka dora masa ba tare da wuce gona da iri ba. Daya daga cikin batutuwan da ya ba wa fifiko dai shi ne kyautata cude-ni-in-cude-ka tsakanin baki da takwarorinsu Jamusawa. A cikin jawabinsa na farko bayan nadinsa da aka yi misalin shekaru biyar da suka wuce Rau cewa yayi, shi ba kawai shugaban Jamusawa ba ne, an nada shi ne domin shugabancin dukkan mutanen dake zaune a kasar Jamus. Kuma bai yi wata-wata ba wajen cika wannan alkawari nasa, inda ya saba kasa kunne domin sauraron kararrakin kowa-da-kowa abin da ya hada har da su kansu bakin. Taken shugabancinsa dai shi ne: Kusantar juna a maimakon rarrabuwa. Kuma yayi bakin kokarinsa wajen cimma wannan buri duk da kasancewarsa ba shugaba ne mai cikakken iko ba. Shugaban mai barin gado mai dadara ba yana mai tofa albarkacin bakinsa wajen sukan lamirin matakan nan na binciken kimiyyar tagwaita halitta. Ya gabatar da shawarwari da dama wadanda suka zama turbar mahawarorin da suka biyo baya akan wannan batu. Johannes Rau kan yi amfani da mukaminsa da kuma ikon da aka tanadar masa domin tsoma baki a mahawarorin da suka shafi makomar kasa da sauran harkoki na yau da kullum. Kuma ko da yake shugaban gwamnati Gerhard Schröder bai gamsu da tsoma baki a mahawarar binciken kimiyyar tagwaita halitta da Rau yayi ba, amma yayi mahrhabin da goyan bayan da ya samu daga shugaban kasar mai barin gado a game da adawarsa da yakin Iraki. Ko sau daya Johannes Rau bai taba nuna son kai ga wani rukuni na siyasar kasar nan a matsayinsa na shugaban kasa ba, ko da yake bai yi fatali da tushensa na dan Socialdemocrats ba. Wannan bankwanan dai tana ma’anar kawo karshen tarihinsa na siyasa ne baki daya, inda ya fara da manufofin kananan hukumomi har ya kai ga mukamin gwamnan jihar Northrhine-Westfaliya, bayan da yayi shekaru 20 cir yana rike da ma’aikatar ilimi ta jihar. Rau ya zama tamkar uban jiha da ya cancanci a yi koyi da shi. An dai sha nanata cewar Jamus kan yi sa’ar nada shugaban kasa kuma ba shakka ana iya tabbatar da wannan batu dangane da Johannes Rau mai barin gado.