A wannan Talata Sarauniyar Holland ke murabus | Labarai | DW | 30.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A wannan Talata Sarauniyar Holland ke murabus

Sarauniya Beatrix ta kasar Holland wadda ke mika ragamar mulki wa danta a wannan Talata, ta yi jawabin ban kwana.

Sarauniya Beatrix ta kasar Holland wadda ke mika ragamar mulki wa danta a wannan Talata, ta gudanar da jawabin ban kwana da madafun iko, sannan ta nemi al'umar kasar su baiwa danta Yarima Willem-Alexander dan shekaru 46 da haihuwa, goyon bayan da ya ke bukata.

Yayin jawabin da aka yada ta kofofin yada labaran kasar, Sarauniyar 'yar shekaru 75 da haihuwa, ta tunatar da al'umar kasar yawan wadanda su ka jagoranci masarautar kasar, ciki harda mahaifiyarta, wadda ta ajiye sarautar a shekarar 1980, domin mika mata, kuma ita ma yanzu ta ajiye domin baiwa danta mulkin tun ya na da kuruciya.

Akwai baki da za su halarci bikin na yau a birnin Amsterdan na kasar ta Holland daga sassa daban daban na duniya. Wannan zai zama Sarki na farko tun fiye da shekaru 100, saboda duk shekarun mata ne ke mulkin masarautar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi