1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

A karon farko likitoci a Amurka sun dasawa mutum kodar alade

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 21, 2024

Likitocin sun shafe tsawon sa'o'i 4 suna tiyatar dasa kodar bayan an jirkita kwayoyin halittarta, ga Richard Slayman mai shekaru 62, da ya jima yana fama da hawan jini da ciwon suga wato diabetes.

https://p.dw.com/p/4dzlO
Hoto: AP Photo/picture alliance

A karon farko likitoci a Amurka sun samu nasarar dashen kodar alade ga wani mara lafiya da ya sha faman jinyar ciwon koda da ke gargarar karshe a babban asibitin birnin Boston na jihar Massachusetts.

Likitocin sun shafe tsawon sa'o'i 4 suna tiyatar dasa kodar bayan an jirkita kwayoyin halittarta, ga Richard Slayman mai shekaru 62, da ya jima yana fama da hawan jini da ciwon suga wato diabetes. Kuma an taba yi masa dashen kodar a shekarar 2018, amma bayan shekaru 5 ta lalace har aka fara yi masa wankin koda.

karin bayani:Trump ba zai yada corona ba inji Likita

Babban asibitin dai ya ce masu fama da ciwon koda sama da dubu daya da dari hudu ne ke jiran aikin dasa musu wata kodar bayan lalacewar ta su.

Karin bayani:Obamacare: Biden ya nuna goyon baya

A baya can an taba yin aikin sanya kodar aladen ga wani mutum da kwakwalwarsa ta mutu, amma na yanzu shi ne aikin farko ga wanda yake raye. Haka zalika an taba dasawa wasu mutane biyu zuciyoyin aladen, amma daga bisani suka mutu kasa da watanni biyu da aikin.