A karon farko Castro ya fito bainar jama'a
August 8, 2010Talla
Tsohon shugaban Cuba Fidel Castro yayi jawabi ga majalisar dokokin ƙasar da ke zama irin sa na farko cikin shekaru huɗu. Mai shekaru 83 a duniya, a shekara ta 2008 ne ya miƙa mulki ga ɗan uwan sa Raul Castro.
A jawabin nasa dai Castro yayi gargaɗi game da ɓarkewar yaƙin nukiliya a duniya tsakanin Iran da Amirka da kuma Isra'ila, muddin Amirka ta kaiwa Iran hari.
Castro yace take-taken Amirka shine ta kaiwa Iran hari, abinda kuma bazai haifar wa yankin gabas ta tsakiya dama duniya baki ɗaya ɗa mai ido ba. Rabon da'a ga Castro a bainar jama'a tun a shekara ta 2006 a sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita:Zainab Mohammed