A farkon watan Nuwamba za a fara shari′ar Mohamamed Mursi | Labarai | DW | 09.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

A farkon watan Nuwamba za a fara shari'ar Mohamamed Mursi

Ana tuhumar tsohon shugaban na Masar da hannu a mutuwar masu zanga-zanga a lokacin wani bore a gaban fadar shugaban a cikin watan Disamban shekarar 2012.

Kafofin yada labarun gwamnatin Masar sun rawaito cewa a ranar 4 ga watan Nuwamba hambararren shugaban kasar Mohammed Mursi zai gurfana gaban kotu bisa zargin angiza magoya bayansa su yi bore. Za a gurfanar da tsohon shugaban ne tare da wasu mutane 14 a gaban kuliya. Ana tuhumarsu da hannu a mutuwar masu zanga-zanga da dama a lokacin wani bore a gaban fadar shugaban kasa a cikin watan Disamban shekarar 2012. A cikin watan Yuli da ya gabata sojojin suka kifar da gwamnatin Mursi na kungiyar 'Yan uwa Musulmi. Tun sannan ne kuma ake tsare da shi a wani wuri da ba sani ba. Su kuma magoya bayan kungiar ta 'Yan uwa Musulmi sun yi ta gudanar da zanga-zangar neman a sake maido da shi kan karagar mulki. A karshen watan Satumba sabbin mahukuntan Masar suka haramta ayyukan kungiyar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu