1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta rufe ofishin kare hakkin dan Adam

Suleiman Babayo
December 6, 2018

Lamuran kare hakkin dan Adam sun tabarbare a kasar Burundi inda aka rufe ofishin hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar.

https://p.dw.com/p/39bWI
Eddy Munyaneza: Lendemains incertains (Uncertain future / Ungewisse Zukunft)
Hoto: Eddy Munyaneza

Gwamnatin Burundi ta bukaci hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta rufe ofishinta da ke kasar, a watannin baya hukumar ta soki mahukunta bisa take hakkin dan Adam da ake samu a kasar ta Burundi.

Mai magana da yawun hukumar ta ce a wannan Alhamis suka samu takarda daga mahukuntan Burundi kan a rufe ofishin na hukumar kare hakkin dan Adam. A farkon wannan shekara ta 2018 shugabana hukumar mai barin gado Zeid Ra'ad al-Hussein ya baiyana Burundi a matsayin kasar da ta yi kaurin suna wajen zubar da jinin dan Adam, bisa matakan cin zarafin al'uma da gwamnatin Shugaba Pierre Nkurunziza ta Burundi ke dauka sakamakon rikicin siyasa da kasar ta samun kanta a ciki.