Ƙungiyar IS na yin barazana ga Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 21.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙungiyar IS na yin barazana ga Gabas ta Tsakiya

Kallamun da firaministan Iraƙi ke'nan Haidar al-Abadi ya bayyana a lokacin wata ziyara aiki da ya kai a Iran.

Haidar al -Abadi ya kuma ce mayaƙan ƙungiyar suna ƙoƙarin raba kawunan musulmi musammum ma'abiya mazabar Shi'a da 'yan Sunni. Wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da firaminista ya kai,tun lokacin da ya kama aiki domin tattaunawa da shugabannin Iran ɗin a kan maganar yaƙi da 'yan ƙungiyar na IS.

Wannan sanarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da aka ba da wani sabon rahoto cewar mayaƙan na Ƙungiyar ta IS sun sake kai hari a garin Kobane.Bayan tun can da farko sun tsere a sakamakon hare-hare na jiragen sama na yaƙi na Amirka na ƙawayanta.