1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin warware rikicin Sudan ta Kudu

June 30, 2014

A shekara ta 2005 ne dai aka cimma rattaɓa hannu a yarjejeniyar sulhu tsakanin Khartum da Juba, wanda aka yi zaton zai kawo ƙarshen yaƙi mafi daɗewa a Afirka

https://p.dw.com/p/1CSit
Südsudan - Abkommen
Hoto: Reuters

A shekara ta 2011 ne dai Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai, sai dai babu alamun zaman lafiya a wannan ƙasa.Rigingimu na cikin gida na jam'iyyar da ke mulki a ƙasar ta Sudan ta Kudu dai ya yi sanadiyyar dubban rayukan mutane, a yayin da wajen miliyan guda suka tsere daga matsugunnensu domin neman mafaka. Batu da ke dasa ayar tambaya dangane da yadda aka kafa tubalin shirin zaman lafiyar wannan ƙasa.

Nazarin masana da ƙwararru a kan rikicin na Sudan ta Kudu

Masana harkokin siyasa da kwararru na danganta wannan matsala da rashin sanya al'ummar ƙasar baƙi cikin tsarin zaman lafiya. A kan haka ne yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu bai yi wani tasiri ba wajen cimma sulhun da ake nema, acewar Jok Madud Jok, wanda ya kafa cibiyar nasarin siyasa a birnin Juba, fadar gwamnatin Sudan ta Kudu:

Machar und Kiir in Addis Abeba
Riek Machar jagoran 'yan tawaye na SudanHoto: Z.ABUBEKER/AFP/Getty Images

"Irin wannan yarjejeniyar da kawai ke sasanta manyan masu gaba da juna, yarjejeniya ce da ba ta da goyon bayan sauran mafi yawan al'ummar ƙasar. Kancewar yarjejeniya ce tsakanin su ɓangarori guda biyu da ke yaƙar juna, inda su kadai ne za su raba albarkatun ƙasa bisa ga wannan yarjejeniya da suka rattaɓa hannu, ba tare da masaniya kan yadda za su warware matsalolinsu na cikin gida ba"

Sai dai har yanzu ɓangarori biyu da ke adawa da juna ba sa muradin wakilcin jama'a. Ko wane ɓangaren na ganin cewar yaƙi ne kadai, zai ba shi damar mallake albarkatun Sudan ta Kudu.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourahman Hassane