Zuma ya yi Allah wadai da hari kan baki
April 16, 2015Jami'an 'yan sandan Afirka ta Kudu sun yi ta harba harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna kyaman baki a birnin Johannesbourg, a daidai lokacin da shugaban kasar Jacob Zuma ya yi kira da a dakatar da irin hare-haren da ake kaiwa baki a kasar.
Kusan mutane 200 ne suka fito suna ihu suna wa baki gargadin cewa su koma kasashensu na asali ko kuma su gamu da gamonsu. Sun yi ta jefa duwatsu a kan motocin dake wucewa kan hanya da ma 'yan sanda a babban birnin cinikayyar kasar.
Shugaban kasa Jacob Zuma ya nuna matukar damuwarsa da wannan lamari ya mayar da martani ga rikicin a majalisar kasar yau da rana.
"Duk yawan takaici, ko fushin da al'umma ta yi, ba zai halatta irin hare-haren da aka kaiwa baki ba, da ma sata da kwasar ganimansu da aka yi. Mun yi Allah wadai da wannan lamari, domin hare-haren sun janyo zubewar martabar da aka san Afirka ta Kudu da shi".