Zuma ya tsallake kuri′un tsigeshi | Labarai | DW | 10.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuma ya tsallake kuri'un tsigeshi

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya a wani kuri'ar yankan kauna da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada da nufin tsige shi daga kan karagar mulki.

Da ban bancin kuri'u shida ne kacal shugaba Zuma ya tsira daga yunkurin tsigeshi daga mulki, babbar jam'iyar adawa a kasar Afirka ta Kudu Democratic Alleince ce ta gabatar da kudurin tsige shugaban sai dai kuri'un ta ba su yi tasirin cimma manufa ba inda ta samu kuri'u 126 na wadanda suka amince da tsige shugaban, ya yinda kuri'u 214 ke nuna kin amincewarsu da raba shugaban da kujerar mulki. Ko da yake ana ganin rinjaye da jam'iyar ANC ke da shi a majalisar ya yi tasiri wajen hana tsige shugaba Zuma.

Wannan dai ba shine karon farko da shugaba Zuma ke sha dakyar daga irin kalubalen da ke bukatar sa da yin murabus ba, a tun shekara ta 2010 shugaba Jacob Zuma ke fama da matsin lamaba na zarge-zargen cin hanci da rashawa da ma karkata dukiyar kasa.