Zuma ya kare kasarsa a kan kyamar baki | Labarai | DW | 27.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zuma ya kare kasarsa a kan kyamar baki

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jakob Zuma ya kare kasarsa daga sukan da kasashen duniya ke yi mata biyo bayan kisan baki 'yan kasashen Afirka da aka yi a kasar.

Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

A cikin wani jawabi da ya gabatar albarkacin samun 'yancin kan kasar Shugaba Zuma ya zargi kasashen Afrika musamman makwabtan kasar tasa da taimakawa wajan yaduwar wanann matsala ta kyamar baki a Afirka ta Kudu, yana mai zargin bakin da kin zama a kasashensu na asali. Shugaba Zuma ya ce wannan batu ne da ya kamata a tattauna a kansa a taron kungiyar kasashen kudancin Afirka ta SADEC dama na kungiyar Tarayyar Afrika AU, a cewarsa 'yan kasashen Afirka da ke kasarsa da dama ne suka bayyana dalillansu na zuwa Afirka ta Kudu da rashin gamsuwa da yanda shugabannin ksashensu ke tafiyar da mulki.