1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma: Barazanar hukuncin dauri

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2021

Masu gabatar da kara a Afirka ta Kudu sun nuna bukatar kotun kundin tsarin mulkin kasar ta daure tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a kurkuku saboda kin zuwa kotu kan shari'ar zargin cin hanci.

https://p.dw.com/p/3pNoR
Südafrika Jacob Zuma
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/A. Ufumeli

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ki bayyana a gaban kotu don ba da sheda kan zargin cin hanci da rashwa da ake tuhumar sa loakcin da ya ke kan gwamnati.

Babbar kotun kasar Afirka ta Kudun dai na zargin Zuma da yin sama da fadi da kudaden baital malin kasar tare da hada kai da wani attijirin dan kasuwa a Indiya aka karkatar da dukiyar kasar a tsawon shekaru 9 da yake mulkin kasar. Sai dai Mr Zuma ya sha musanta wadannan zarge.-zargen.

Ana sa ran zuwa kowane lokaci alkalin da ke shari'ar hzai sanar da maatki na gaba sakamakon rashin halartar Jacob Zuma zaman kotun na yau, duk da cewa lauyan da ke kare shi ya gabatar wa kotun wasikar rashin halartar Zuma tare da cewa sammacin baya kan tsari.