1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: An fara bincikar Zuma

Abdul-raheem Hassan
July 15, 2019

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai bayyana a gaban kwamitin bincike domin amsa tambayoyi kan zargin cin hanci, da ya janyo salwantar makudan kudin kasar a lokacin mulkinsa.

https://p.dw.com/p/3M4oc
Südafrika Prozess gegen Jacob Zuma in Durban
Hoto: Reuters/N. Bothma

Al'ummar kasar ta Afirka ta Kudu dai sun sa ido a akwatunan talabijin domin ganin da kuma sauraren jawaban da tsohon shugaban zai yi wa kwamitin domin kare kansa daga zargin.

Zargin cin hancin ne dai ya yi sanadiyyar yin awon gaba da kujerar mulkinsa, zargin kuma da ya sha karyatawa duk kuwa da wasu shaidu daga jami'an gwamnati na alakanta shi da yin sama da fadi da dukiyar kasar.