Ziyarar Trump katangar yammacin Kudus. | Labarai | DW | 22.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Trump katangar yammacin Kudus.

Shugaban Amirka Donald Trump ya kai ziyara katangar yammacin birnin Kudus da ke zama wuri mafi tsari na mabiya addinin Yahudu.

Shugaban Amirka Donald Trump ya kai ziyara mai tarihi katangar yammacin birnin Kudus da ke zama wuri mafi tsari na mabiya addinin Yahudu.

Trump wanda ya dafa katangar domin tabarraki ya kasance shugaban Amirka na farko a karagar mulki da ya ziyarci katangar.

Sanye da bakar hula kokuwa cikin tsatsauran matakan tsaro da rakiyar babban limamin Yahudawa na wurin ibadar, Trump ya baiyana gamsuwa da karramawar.

Yace Ina alfahari da zuwa na nan. An sanar da ni cewa ni ne shugaba na farko mai ci da ya kawo ziyara wannan katanga ta yammacin kudus, babbar karramawa ce kuma ina godiya matuka.