Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a wasu kasashen Afirkya ta dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a wasu kasashen Afirkya ta dauki hankalin jaridun Jamus

Sabani tsakanin shugabannin Yuganda da Ruwanda ya jefa rayuwar mutane ya jefa rayuwar mutanen kasashensu cikin mawuyacin hali kana Aliko Dangote shamshakin mai arzikin Najeriya na kara karfafa.

Jaridar Die Welt da ta yi tsokaci kan ziyarar aiki da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai wannan mako a kasashen Afirka ta Kudu da Angola. Jaridar ta ce a wannan karo batun baki haure bai dauki hankali ba a ziyarar Merkel a Afirka. Ta ce Afirka ta Kudu da Angola ba su da wani adadi na a zo a gani na 'yan kasashensu da ke kaura zuwa Turai.

Saboda haka batun bunkasa tattalin arziki a kasashen biyu da ma a nahiyar Afirka gaba daya ya kasance sama a jadawalin ziyarar, musamman kasancewa a bana shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa zai shugabancin kungiyar tarayyar Afirka. Jamus na zama abokiyar kasuwanci mafi muhimmanci ga Afirka ta Kudu, inda kamfanonin Jamus kimanin 450 ke aiki a kasar.

Sabani tsakanin shugaban Yuganda Yuweri Museveni da shugaban Ruwanda Paul Kagame ya jefa rayuwar da yawa daga cikin al'ummomin kasashensu cikin mawuyacin hali, amma yanzu sun yi alkawarin kyautata hulda, inji jaridar Die Tageszeitung. Ta ce ba wata masafaha ce ta abokantaka ba, kamar yadda ya fito fili a hoton karshen taro. Shugabannin Afirka hudu a kusa da juna sun yi masafaha cikin murmushi, amma Museveni da Kagame da suka halarci wani taron sasanta tsakaninsu, ba su tsaya  kusa da juna ba, a tsakaninsu akwai shugaban Kwango Felix Tshisekedi da shugaban Angola Joao Lourenco a taron sulhun da ya gudana a birnin Luanda na kasar Angola.

Ruwanda da Yuganda sun yi alkawarin sakin firsinonin siyasa, ba kuma za su yi ta wa juna zagon kasa ba, sannan za su mutunta hakin dan Adam. Tun a bara ne ake kai ruwa rana tsakanin kasashen biyu na yankin gabashin Afirka, abin da ya jefa rayuwar 'yan kasashen cikin halin ni 'ya su. A watan Maris Ruwanda ta dauki matakin rufe kan iyakokinta da Yuganda. Ita kuma Yuganda ta katse wutar lantarkin da take ba wa Ruwanda. Kasashen biyu na zargin juna da mara wa 'yan adawa da 'yan tawaye baya.

Mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka na kan hanyar cimma buri. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga game da hamshakin dan Najeriya Aliko Dangote da ta ce baya ga manyan-manyan kamfanoni da ya mallaka, har yanzu bai yi kasa a gwiwa ba, domin nan ba da jimawa ba zai zama abin sha'awa ga masu son kwallon kafa. Jaridar ta ce Dangote da bincike ya nuna shi ne a matsayi na 96 a jerin hanshakan attajirai na duniya, amma na farko a Afirka, an kiyasta dukiyarsa ta kai dala milyan dubu 15.

Rahotanni sun nunar cewa yana son ya fadada harkokinsa zuwa kasashe masu arzikin masana'antu don kare dukiyarsa daga yawan faduwar darajar takardun kudin Najeriya wato Naira. Hakazalika Dangote ko da yake ba mai sha'war kwallon kafa ba ne, amma yana da muradin sayen kungyiar kwallon kafa ta Ingila wato Arsenal, inda ma aka ji shi yana cewa idan ya kammala wasu aikace-aikace da ke gabansa, a badi yana iya sayen kulob din na Arsenal. Wato ke nan yanzu al'umma a Turai za su kara sanin wannan attajiri dan Afirka.

Sauti da bidiyo akan labarin