Ziyarar shugaban Jamus a Ehiopiya | Labarai | DW | 17.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaban Jamus a Ehiopiya

Shugaba Joachim Gauck na Jamus zai shafe kwanaki hudu ya na tattaunawa da hukumomin Habasha game da al'amuran kare hakkin bil Adama da kuma mulkin demokaradiya.

default

Gauck zai ziyarci Afirka a karon farko

Shugaban Tarayyar Jamus Joachim Gauck zai fara wata ziyarar aiki na kwanaki hudu a wannan lahadin a kasar Ethiopiya. Wannan dai shi ne karon farko da shugaban zai ya da zango a nahiyar Afirka tun bayan da ya dare kan wannan kujera mai alfarma.

Daga cikin mahimman batutuwa da zai mayar da hankali akai har da dangantaka tsakanin musulmi da kiristocin wannan kasa da kuma batun kare hakkin bil Adama. Ranar litinin ne zai yi jawabi inda zai nuna mahimmacin kare hakkin mata da kuma gudanar da mulkin demokaradiya a Ethiopiya. Ziyarar ta shugaban Jamus a Addis Abeba da ke zama cibiyar Kungiyar Gamayyar Afirka ta zo ne a daidai lokacin da AU ke shirye shiryen bikin cika shekaru 50 da kafuwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar