Ziyarar shugaban ƙasar Jamus a Bethlem | Siyasa | DW | 01.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar shugaban ƙasar Jamus a Bethlem

Christian Wulff da Mahmud Abbas sun gana game da batun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

default

Christian Wulff da Mahmud Abbas

A ƙarshen  ziyarar   da ya kai  yankin Gabas ta Tsakiya, shugaban ƙasar Jamus Christian Wulff   tare da babbar murya ya baiyana goyon bayansa ga tsarin samarwa Palesdinawa  ƙasar   kansu inda za su zauna kafaɗa da kafaɗa da Isra´ila.  Samun zaman lafiya mai ɗorewa da zai gamsar da kowa da kowa,  ba zai tabbata ba, sai ta hanyar samarwa Palesdinawa yantacciyar ƙasar da yantacciyar ƙasar Israila, inji shugaban na Jamus,  lokacin jawabin  haɗin gwiwa gaban manema labarai tare da shugaban Paledinawa, Mahmud Abbas a Bethlehem. Yace a shawarwarin siyasa  da tattaunawar da   yayi  tun daga yan kwanakin baya ya gano cewa:

Zaman lafiya  abu ne mai iya samuwa, idan har  duka waɗanda abin ya shafa su ka nuna ƙwarin zuciya da  niyyar cimma zaman lafiyar. Ina ganin wata kyakkyawar dama ce idan  haɗin kai tsakanin waɗanda suke da hannu a wananan rikici ya zama a'ala kan  ci gaba da   fuskantar   rikici a yankin, idan duka masu hannu a cikin sa,  da suka yi  fiye da shekaru 4000 suna   faɗa da juna suka yanke shawarar fuskantar alƙibla guda, yadda kowa zai cimma burin sa.

Wulff ya yabawa aiyukan  hukumomin Palesdinawa da ke samun taimakon kuɗi daga Jamus. Ƙasar dai ta na bada gudummuwa a fannin giggina   aiyukan mulkin yankunan na Palesdinawa da  hora da yan sanda da aiyukan shari'a da bada ilimi a makarantu, kamar yadda shugaban na Jamus ya nunar. Mahmud Abbas, wanda tun da farko ya  yi marhabin da bakon daga Jamus tare da faratin soja a fadar sa dake Bethlehem, ya kwatanta Wulff  a matsayin aboki na-gari, ya kuma godewa Jamus saboda taimakon da take baiwa hukumar sa.

Ya ce mu Palesdinawa muna godiya ga dukkanin ƙoƙarin da ku ke yi bisa ganin ci gaban Palesdinawan, muna kuma godiya ga dukkan Jamusawa, saboda duka irin abubuwan da suke yi mana.

To  sai dai  shugaban  na Palesdinawa ya janye jikin sa daga karfin zuciyarda shugaban Jamus ya nuna, musmaman bisa lura da   shawarwarin neman zaman lafiya tare da Israila wadanda yanzu watanni biyu kenan da aka dakatar dasu. Yace idan  ba tareda Israila ta dakatarda  shirin ta na giggina matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye ba,  na yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Kudus, ba zai yiwu a koma zauren shawarwarin ba.

A bisa amsa tambaya fdaga wani dan jarida na Palesdinawa, shugaba Christian Wulff ya maimaita  alhakin  dake wuyan Jamus na  tabbatar da tsaron Isra´ila, to amma yace Jamus ta na da nauyi na musamman  a kanta a game da Palesɗinawa. Shugaban na Jamus  yayi kira ga dukkanin Jamusawa su kai ziyara a birnin Bethlehem, dake yankin dake karkashin mulkin  Palesɗinawa a yanzu.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Zainab Mohamed Abubakar