Ziyarar shugaba Obama a Kyuba | Labarai | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugaba Obama a Kyuba

Shugaba Obama ya ce wannan ziyara ce ta tarihi da za ta bude tarihi na damarmaki tsakanin kasashen biyu a harkokin tattalin arziki da kasuwanci.

Kuba Havana Staatsbesuch US Präsident Obama

Shugaba Obama da iyalansa da saukarsu a Kyuba

Shugaba Barack Obama na Amirka ya kafa tarihi inda ya fara ziyararsa a kasar Kyuba ranar Lahadi, abin da ya kawo karshen gwamman shekaru da aka samu kafin ganin wani shugaban kasar Amirka ya sanya kafarsa a wannan kasa da aka dade ana zaman doya da manja tsakanin juna.

Da sanya kafarsa a wannan kasa ta Kyuba bayan da a shekara ta 19 88 wani shugaba na Amirka ya ziyarci wannan kasa, shugaba Obama ya ce wannan ziyara ce ta tarihi da za ta bude tarihi na damarmaki tsakanin kasashen biyu.

A ranar Litinin din nan ce dai shugaba Raul Castro zai bayyana a fadar juyin juya hali ta kasar ta Kyuba dan gaisawa da shugaba Obama bayan da a jiya lokacin da shugaban ke sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Jose Marti tare da mai dakinsa Michelle Obama da 'ya'yansa Malia da Sasha ba a ganshi ba sai wasu manyan kusoshi na gwamnati.