Ziyarar Shugaba Macron a kasashen Afirka | Siyasa | DW | 27.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Shugaba Macron a kasashen Afirka

Shugaba Emmanuel Macron zai gudanar da wani rangadinsa na farko a wasu kasashen Afirka inda zai soma da birnin Ouagadougou na Burkina Faso, sannan ya je kasar Cote d'Ivoire da Ghana.

Daga wannan Litinin zuwa ranar Alhamis, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron zai gudanar da wani rangadinsa na farko a wasu kasashen Afirka inda zai soma da birnin Ouagadougou na Burkina Faso, sannan ya je kasar Cote d'Ivoire da kuma Ghana a wani mataki na tallata siyasarsa kan kasashen Afirka da ya ce za ta mayar da hankali kan harkokin kasuwanci da ci gaban matasa da harkokin ilimi. Macron zai yi amfani da wannan dama domin farfado da martabar Faransa a idanun 'yan Afirka.

Shi dai shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kuduri aniyar yin komai daidai. Yana son ya dawo daga rakiyar manufofin siyasar magabatansa dangane da Afirka, inda tuni ya kafa wani kwamitin mashawarta na mutum 11 da suka hada da 'yan kasuwa masu asali da nahiyar Afirka.

Zai fara wannan ziyara mai muhimmanci a kasar Burkina faso inda shugaban na Faransa zai yi wani jawabi a gaban dalibai 800 na jami'ar Ouagadougou babban birnin kasar, kuma a nan ne zai sanar da tsarinsa na hulda da kasashen Afirka, tare da isar da sako ga matasan na Afirka a cewar fadar shugaban na Faransa ba tare da bada wani karin haske ba.

Guyane - Emmanuel Macron und französischer Bildungsminister Jean-Michel Blanquer in Maripasoula (Reuters/A. Jocard)

Makomar matasa abin so ga Macron

Tumba Shango Lokoho masanin kimiyyar siyasa ne dan kasar Kwango da ke koyarwa a jami'ar Sorbonne da ke birnin Paris da ya bayyana sabbin manufofin na Shugaba Macron da wani sako kwakkwara:

"Idan matasan Afirka su ne makomar nahiyar, to fa suna bukatar tallafi ta yadda za su samu ilimi da bude musu kofofin samun aikin yi a nahiyar domin ciyar da wannan nahiya gaba."

Ga Antoine Glaser dan jaridar Faransa kuma mawallafi a fili yake cewa Shugaba Macron na son a jawo matasan Afirka kusa da shi to amma hakan ba mai sauki ba ne.

"Faransa ta kwashe tsawon shekaru tana aiki da wasu manufofi kan Afirka da ba su dace ba. Shi ya sa yanzu ake neman canji. Sai dai shugabannin Afirka da suka dade kan karagar mulki na zama manyan abokan dasawar Faransa. Amma Emmanuel Macron na son ya dawo daga rakiyar wannan al'ada inda zai nuna karara ya damu da bukatun masatan wannan nahiya da kuma 'yan Afirka da ke ketare."

Frankreich Präsident Emmanuel Macron in Clichy-sous-Bois (picture-alliance/MAXPPP/Hamilton)

Matasan Afirka da ke Turai na da rawar takawa a tsarin Macron

Bayan watanni shida kan karagar mulki an fara ganin alamun farko cewa dangantaka za ta iya canjawa inji Tumba Shango Lokoho masanin kimiyyar siyasa. Ya ce Macron na bin manufofi na girmamawa da kuma fayyace gaskiya da takwarorinsa na Afirka, inda a ziyarar farko da ya kai kasar Mali ya fito karara ya ce huldar dangantaku na bukatar sabon ginshiki.

Samun sabbin bangarori na tattali arziki na zama wani buri na shugaban, musamman dangane da damarmakin samun aiki a yankin Yammacin Afirka. A karshen mako Macron zai gane wa idonsa wani shirin tallafa wa masu son kafa kananan kamfanoni a Ghana, da masharhanta suka ce ziyara ce da za ta yi babban tasiri.

Sauti da bidiyo akan labarin