Ziyarar shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya na ci gaba da shan suka | Siyasa | DW | 27.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya na ci gaba da shan suka

Ba zato ba tsammani ne dai shugaban wanda ya shiga damara irin ta soji tare da samun rakiyar wasu daga cikin manyan hafsoshin tsaron kasar, ya ziyarci garuruwan na Baga da Mubi a jihohin Borno da Adamawa.

Al'ummar yankin Arewa maso gabashin Najeriya na tofa albarkacin bakin su kan ziyarar ba zata da shugaban ya kai wasu garuruwa da rundunar tsaron Najeriya ta yi ikirarin kwatowa daga hannun mayakan Boko Haram a jihohin Borno da Adamawa.

Ba zato ba tsammani ne dai shugaban wanda ya shiga damara irin ta soji tare da samu rakiyar wasu daga cikin manyan hafsoshin tsaron kasar ya ziyarci garuwan Baga da Mubi a jihohin Borno da Adamawa.

Kamerun Flüchtlingslager Minawao

Rayuwa cikin kunci a yankin da Boko Haram ta kama

A cewar shugaba Jonathan, ziyarar ta karfafa gwiwa ce ga dakarun kasar wanda ya hakikance cewa suna samun nasara a kokarin da suke yi a kwato sauran garuruwar da suka fada hannun mayakan Kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna da aka fi sani da Boko haram nan da makonni hudu da ke tafe wato lokutan babban zaben kasar.

Duk da cewa an yi yadda aka saba wato gudanar da ziyarar ba tare da manema labarai ba, akwai hotuna da aka fitar wanda ke nuna shugaban tsakanin wasu sojoji da aka ce a garin Baga ne da kuma wasu hotunan da ke nuna shi a fadar sarkin Mubi da kuma wadan aka dauka yayin da ya ke samun tarba daga gwamnaonin jihohin Borno da Adamawa a filin tashi da saukar jiragen sama na Borno.

Nigeria Baga 2013

Rayuwa cikin fargabar rashin tsaro a arewa maso gabas

Wasu dai na ganin matakin shugaban a matsayin na siyasa ganin bai taba zuwa jajanta wa al'umma hasarar rayuka ba sai a wannan lokacin da ake shirin yin zabe na kasa baki daya.

Suma masu fashin baki kan harkokin yau da kullam sun bayyana ziyarar ba zatan suka yi da ihu bayan hari.

Sauti da bidiyo akan labarin