Ziyarar minista Müller na Jamus a Najeriya | Labarai | DW | 10.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar minista Müller na Jamus a Najeriya

Harkokin kasuwanci da raya kasa da kuma tattaunawar samar da zaman lafiya ne za su mamaye ziyarar da ministan raya kasa na Jamus zai gudanar a Abuja da kuma Lagos.

Ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Müller zai gudanar da ziyarar aiki a wannan Talatar a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya da kuma Lagos cibiyar cinikayyar wannan kasa . Ajendar babban jami'in gwamnatin Jamus ta tanadi tattaunawa da bangaren gwamnati da manyan 'yan kasuwa da shugabannin addinai da na kungiyoyi masu zaman kansu a biranen biyu. Hakazalika mista Müller zai mayar da hankali kan ayyukan raya kasa da tarayyar Jamus ke gudanarwa a tarayyar Najeriya.

Ziyarar ta ministan raya kasashe maso tasowa na Jamus ta zo ne a daidai lokacin da Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, ta ke ci gaba da fafutuka da makamai inda ta ke kai hare-hare a wasu jihohi na Najeriya. Ita dai kungiyar ta na sukan lamarin duk wani tsarin rayuwa na kasashen yamma ciki kuwa har da karatun Boko, inda maimakon haka ta ke nema a kafa shari'ar musulunci a arewacin kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a najhiyar Afirka. Akalla mutane dubu da 500 ne dai suka rasa rayukansu cikin watanni shida na baya-bayannan a Najeriya sakamakon hare-haren da Boko Haram ta kai musamman ma a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Usman Shehu Usman