Ziyarar Macron ta farko a Afirka | Siyasa | DW | 19.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Macron ta farko a Afirka

Mali dai ita ce kasa ta farko da Macron ya fara ziyarta a nahiyar Afirka kuma a wannan ziyara shugaban ya yi tattaki zuwa yankin Gao don tattaunawa da sojojin Faransa da ke kasar.

Wannan ziyara ta Shugaba Macron na a matsayin wani mataki na jaddada aniyar kasarsa ta ci gaba da yakin da ta ke da 'yan jihadi na yankin Sahel ta yadda tsarin zai kasance cikin kyakyawar hulda da kasar Jamus. Sai dai cikin wata hira da aka yi da shi sabon shugaban na Faransa na ganin sake salon hulda da kasashen Afirka shi ne abun yi nan gaba inda ya ke cewar "muna da nauyin da ya rataya a kanmu na samar da tsaro ta hanyar hulda da sauran kasashe da kungiyar tarayyar Afirka, da kuma hulda tare da rundunonin sojojin Afirka."

Yankin Arewacin kasar ta mali dai ya fada a hannun kungiyoyin 'yan ta'adda a watan Maris zuwa Afrilu na 2012 wadanda hadin gwiwar sojojin kasa da kasa bisa jagorancin sojojin kasar Faransa suka koresu a shekara ta 2013. Sai dai kuma har yanzu akwai yankunan da basa hannun sojojin kasar ta Mali da na Faransa da ma Majalisar Dinkin Duniya da a kullu yaumin ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda. Etienne Fakaba Sissoko shugaban cibiyar nazarin kimiyyar siyasa da tattalin arziki a kasar ta Mali ya ce ya kyautu shugaban na Faransa ya dauki matakai na gari kan makomar birnin Kidal a arewacin kasar ta Mali.

Kungiyoyin kare hakin jama'a kamar su Human Rights Watch sun soki yadda kasar ta Mali ke ci gaba da dauwama cikin rishin kwanciyar hankali tare da yin kira ga sabon shugaban na Faransa Emmanuel Macron da ya yi kira ga shugaban na Mali da ya dukufa kan manyan dalillan da suke haifar da rashin zaman lafiya a kasar musamman ma rishin karfin iko da cin hanci da rashawa da ma cin zarafin jama'a da sojojin kasar ke yi.

     

     

Sauti da bidiyo akan labarin