Ziyarar John Kerry a Berlin | Labarai | DW | 26.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar John Kerry a Berlin

Jamus da Amirka sun ce suna buƙatar yarjejeniyar kasuwanci mara shinge a tsakaninsu cikin gaggawa bayan da hukumomi suka gana da sakataren kula da harkokin wajen Amirka

Jamus da Amirka sun bayyana buƙatar samar da yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba a tsakaninsu cikin gaggawa. Ana sa ran ƙaddamar da tattaunawa dangane da wannan batu cikin bazara kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya bayyana, bayan da ya gana da takwararsa na Amirka John Kerry wanda ke rangadi a nan Turai. Ministocin biyu sun yi bayani kan yadda ya kamata a rage kuɗin ruwa tsakanin Amirka da Turai ta yadda ɓangarorin biyu za su bunƙasa tattalin arzikin ƙasashensu su kuma samar da ayyukan yi ga 'yan ƙasa. sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi ƙarin bayani..

"Jamus ce babbar abokiyar kasuwancinmu a Turai, kuma muna so mu ga ƙarin harkokin kasuwanci da na zuba jari, wadanda zasu samar da ayyukan yi, ayyukan yi wa Jamusa da Amirkawa da ayyukanyi wa Turawa.

Mr. Kerry ya yada zango ne a birnin Berlin a cikin ziyarar ran gadin da ya ke yi a Turai bayan da ya kama aiki a sabon muƙaminsa na sakataren kula da harkokin wajen Amurka.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Saleh Umar Saleh