1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Biden ya jaddada bukatar zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
April 12, 2023

Shugaba Joe Biden ya nemi duk bangarorin da ke tayar da jijiyoyin wuya a Ireland ta Arewa da su daidaita tsakaninsu gudun mayar da hannun agogo baya.

https://p.dw.com/p/4PyQY
Shugaba Joe Biden a birnin Belfast
Shugaba Joe Biden a birnin BelfastHoto: Clodagh Kilcoyne/REUTERS

Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya ce, kada Ireland ta Arewa ta yi sake, rikicin siyasa ya kara tayar da fitinan da ka iya shafar zaman lafiyan kasar. Biden ya fadi hakan ne a yayin da ya ke jawabi a wata jami'a a Belfast babban birnin kasar, a lokacin bikin cika shekaru 25 da cimma yarjejeniyar da ta kawo karshen tashin hankalin da aka shafe shekaru da dama ana yi, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, kafin daga bisani Amirka ta shiga tsakani a cimma yarjejeniyar da ta kawo wa kasar zaman lafiya. 

A baya-bayan nan, an samu rashin jituwa a tsakanin Ireland ta Arewa da Britaniya kan cinikayya, bayan ficewar Britaniyan daga cikin Tarayyar Turai da kuma rikicin jam'iyyun siyasa na cikin gida da ake fargabar ka iya tayar da zaune tsaye a kasar. Shugaban Biden da ke ziyara a nahiyar Turai dai, ya yi tattaki ya zuwa kasar albarkacin bikin da kuma rawar da kasarsa ta taka wurin samar da zaman lafiya.