Zimbabwe ta yi wa kamfanonin Amirka da Birtaniya barazana | Labarai | DW | 25.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabwe ta yi wa kamfanonin Amirka da Birtaniya barazana

Mugabe ya ce zai yi ramuwar gayya in Amirka da Birtaniya suka ci gaba da matsa masa lamba ko yunkurin kakaba masa takunkumi.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya ce gwamnatinsa za ta dauki mataki kan kamfanonin Birtaniya da Amirka da ke kasarsa in har gwamnatocin kasashen suka ci gaba da matsa masa lamba ko ma sanya masa takunkumi.

Mugabe ya ce muddin suka ci gaba da abinda suke to kasarsa za ta yi ramuwar gayya kan kamfanonin da Birtaniya da na Amirka wanda ya ce suna harkokinsu a kasar yanzu haka ba tare da gwamnatinsa ta sanya musu idanu ba ko gindaya musu wasu sharruda ba.

Shugaban dan shekaru 89 da haihuwa na wadannan kalamai ne daidai lokacin da ake cigaba da sukar zaben da yai sanadiyyarsa komawa mulki karo na bakwai wanda 'yan adawa da sauran kasashe ke cewar ya na cike da mugadi, sai dai jam'iyyar Mugabe ta Zanu-PF ta musanta wannan zargi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Nasiru Awal