1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabwe ta cika shekaru 33 da samun 'yancin kai

April 18, 2013

Lokacin bukin cika shekaru 33 da samun 'yancin kan, shugaba Robert Mugabe ya gargaɗi ƙasashen ƙetare kan shiga al'amuran da suka shafi ƙasarsa

https://p.dw.com/p/18J04
ARCHIV - Der Präsident von Simbabwe, Robert Mugabe, gibt am 17.01.2013 in Harare, Simbabwe, eine Pressekonferenz. Mugabe will auch nach 33 Jahren weiter an der Macht bleiben. Foto: Aaron Ufumeli/epa/dpa (zu dpa "Simbabwe stimmt über Verfassung ab: Mugabes Machtwille ungebroche" vom 15.03.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Robert MugabeHoto: AFP/Getty Images

A Ƙasar Zimbabwe, lokacin bukin zagayowar ranar da ta sami 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka yau shekaru 33, shugaban ƙasa Robert Mugabe ya ce ƙasarsa ba zata amince da abun da ya kira katsalandan daga ƙasashen ƙetare lokacin zaɓukan da ƙasar ke shirin gudanarwa a ƙarshen wannan shekarar ba.

Mugaben ya bayyana hakan ne a wani gajeren jawabin da ya gabatar a babban birnin ƙasar wato Harare, inda ya haƙiƙance kan cewa, ƙasarsa ba zata bar ƙasashen ƙetare su kasance cikin masu sanya ido a zaɓukan ba, masu sanya ido zasu kasance daga ƙasashen Afirka ne kaɗai.

"Ba zamu taɓa amincewa da katsalandan ba, a dalilin haka ina kira ga waɗannan ƙasashe da su gudanar da ayyukansu da ma duk wata dangantaka da ƙasarmu bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa ta yadda zamu yi cuɗanyar da zata amfane mu".

A baya dai an zargi shugaba Mugabe da haddasa tashe-tashen hankula da kuma firgita masu adawa amma a wannan karon shugaban ya gargaɗi 'yan ƙasa da su yi zaɓe cikin lumana idan lokacin ya zo

"Ina kira ga 'yan ƙasa da su maimaita yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ya kasance a lokacin da muka jefa ƙuri'ar raba gardama, kuma mu guji haddasa tashe-tashen hankula"

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi