Zimbabuwe: Za a binne Mugabe a makabartar gwarzayen kasar | Labarai | DW | 13.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zimbabuwe: Za a binne Mugabe a makabartar gwarzayen kasar

Za a girmama tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe, inda za a binne gawarsa a makabarta da ake rufe gwarzayen kasar da ke birnin Harare.

Rahotanni daga Harare babban birnin kasar Zimbabuwe na cewa an bayyana inda za a binne marigayi shugaban kasar, inda za a rufe gawar a makabartar gwarzayen kasar da ke Harare, a cewar iyalansa ta bakin Leo Mugabe.

Leo Mugabe ya kara da cewa har yanzu suna jiran shugabanninsu na gargajiya su tabbatar da lokacin da za a yi jana'izar da ma ko za a yi ta a asirce ne ko kuma a bayyanar jama'a. 

Wannan bayanin na zuwa ne bayan wata jayayya da ta kaure tsakanin mahukuntan kasar da iyalan shi Mr. Mugaben, a kan inda za a binne shi.

Gwamnatin ta so ta girmama shi da binne shi a makabartar da aka tanada don gwarzaye amma su kuma iyalan suka ce za su so su cika masa burinsa na binne shi kusa da mahaifiyarsa a garinsu da ke da nisan kilomita 85 daga Harare.

Marigayi Mugabe ya rasu ranar Juma'ar da ta gabata yana da shekaru 95.