1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa mafi muni a Afirka ta janyo asarar rayuka

March 20, 2019

Har yanzu ana cigaba da samun karin wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar mummunar guguwa mai suna IDAI da ma zabtarewar kasa da batsewar koguna

https://p.dw.com/p/3FMRB
Rettungseinsätze nach Wirbelsturm «Idai»
Hoto: picture-alliance/AP/T. Mukwazhi

Tun bayan mummunar guguwar nan mai lakabin IDAI da ta hallaka daruruwan mutane a wasu kasashen kudancin Afirka, har yanzu al'ummar yankin Chimanimani da ke gabashin Zimbabwe na a matsayin inda bala'in ya fi muni sakamakon mutuwar mutane kusan dari da asarar tarin dukiya.

Fanuel Ngwacheni ya bayyana kaduwarsa yayin jana'izar sirikinsa mai suna Morgan Dube mai shekaru 83, da wannan iska mai karfi ta hallaka.Yana mai jaddada jimaminsa da wannan rashi.

Marigayi Dube daya dai daga cikin mutanen da suka mutu sakamakon zamewar laka a yankin na Chimanimani mai tuddai da dama, wanda har ya zuwa wannan lokaci mazauna garin ke cikin halin dimuwa da firgicin faruwar iftila'in da zai dade a zukatunsu.

Chipo Dhilawo dai wata uwa ce da ta rasa 'ya'yanta biyu mata masu shekaru 4 da 8 da haihuwa, yanzu haka dai ta samu kanta a matsugunin da hukumar ba da agajin gaggawa ta samar a kasar inda suka rakabe tare da ci gaba da jimami.

Simbabwe Wirbelsturm «Idai»
Irin sarar da guguwar ta janyoHoto: Getty Images/AFP/Z. Auntony

Ayar tambayar da ke fitowa daga bakunan mutane ba ta wuce irin ko ina aka kwana kan irin matakan da hukumomi ke dauka don magance halin da jama'a ke shiga a sakamakon aukuwar masifu irin wannan ba.

Birgediya Janar Joel Muzvidziwa shi ne jagoran rundunar sojin da ke aikin ceto wadanda bala'in ya shafa, ya yi karin haske kan yadda aikin agajin ke gudana.

Ya ce "Girman bala'in ya wuce gaban misali, muna kuma fuskantar kalubalen sauyin yanayi, da a ce jirage masu saukar ungulu cikin gaggawa da komai ya tafi cikin sauki."

Tabarbarewar halin da titunan garin suka shiga gami da rashin kyawun layukan waya ya kara kawo tarnaki cikin aikin ceton. Haka zalika karyewar gadoji ma wani cikas ne da ya hana isar kayan taimako yankin, hakan ya tilasta amfani da jirage masu saukar ungulu.

Rettungseinsätze nach Wirbelsturm «Idai»
Agajin gaggawa ga wadanda suka jikkataHoto: picture-alliance/AP/T. Mukwazhi

 A Talatar makon nan aka fara kwashe masu neman taimakon da jirage masu saukar ungulu, to amma likitoci sun nuna damuwa matuka kan irin halin da mutanen ke ciki sakamakon tsawon lokacin da suka shafe ba tare da rabauta da wani taimakon ma'aikatan lafiya ba. Themba Dhilawayo guda ne daga cikin likitocin da ke aikin taimakon.

Ya ce "Daga cikin wadanda muka samu damar dubawa da raunukansu suka fi tsanani su ne wadanda kawunansu suke fashe da masu karaya a hannaye da kafafuwa. "

Za dai a jima ana tuna irin wannan mummunan iftila'i musamman ma a wannan yanki na Chimanimani da ke Zimbabwe, kuma wani abin yabawa shi ne yadda al'ummar garin ke bada taimako ga asusun da aka kafa don ceto jama'ar.