1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwach din Real Madrid ya kamu da corona

Abdourahamane Hassane
January 22, 2021

Tsohon shahararan dan wasan kwallon kafa na na Faransa wanda ke rike da matsayin mai horas da 'yan wasan  klub Real Madrid na Spain  Zinedine Zidane ya kamu da cutar corona

https://p.dw.com/p/3oIL2
Champions League - Juventus v Olympique Lyonnais | Tor Memphis Depay
Hoto: Reuters/P. Powel

A cikin wata sanarwa da klub din na Madrid ya bayyana ya ce bayan da aka yi masa gwaji an gano cewar yana dauke da kwayoyin cutar ta corona. Babu dai wani karin bayyani da klub din na Madrid ya yi bayan wannan sanarwa sai dai kungiyar 'yan wasan na Madrid ta ce za ta yi taron manema labarai a nan gaba.