1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin magudi a zaben Madagaska

Gazali Abdou Tasawa
November 8, 2018

A kasar Madagaska tsohon shugaban kasar Henry Rajaonarimampianina daya daga cikin 'yan takara 36 da suka fafata a zaben shugaban kasa na jiya Laraba, ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai da dama a cikin zaben. 

https://p.dw.com/p/37vMs
Madagaskar, Antananarivo: Wahlen des Präsidenten
Hoto: picture-alliance/AP/K. Dhanji

Rajaonarimampianina wanda sakamakon farko na zaben na cibiyoyin zabe 358 da hukumar zaben kasar ta bayyana a wannan Alhamis ya nunar da cewa abokan hamayyarsa Marc Ravalomanana da Andry Rajoelina sun yi masa fintikau ya ce an aiki da rijistan zabe maras inganci da kuri'un da aka rigaya aka sa wa hannu tun kafin a yi zaben, kana an rika yi wa magoya bayansa barazana. Rajaonarimampianina ya ce ba za su taba bari ba a kwace wa al'umma zabin da ta yi, lamarin ya soma haifar fargabar yiwuwar samun rikicin bayan zaben.