1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fulgence Kayishema ya gurfana a gaban kotu

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2023

Bayan da ya kwashe shekaru 20 yana 'yar buya, daga karshe mutumen nan da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen kisan kiyashi a Rwanda, ya gurafa gaban kotu.

https://p.dw.com/p/4RrZU
Fulgence Kayishema appears in the Cape Town Magistrates Court
Hoto: Nic Bothma/REUTERS

Mutumen nan da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen kisan kiyashin Rwanda a shekarar 1994, ya gurfana a wannan Jumma'ar a gaban kotu, a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Fulgence Kayishema, ya shiga hannun hukuma ne a makon jiya, bayan da ya shafe shekaru 20 yana kuli-kurciya da mahukunta da ke cewa ya yi ajalin fiye da mutane dubu biyu a wata majami'ar da ke yankin Nyange, na Arewa maso gabashin Rwanda.

Alkalan kotun na Majalisar Dinkin Duniya na tuhumarsa da zama silar kone majami'ar da 'yan gudun hijira ke samun mafaka.