1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin kashe fararen hula a yakin Mali

February 1, 2013

Amnesty International da Human Right Watch sun fitar da rahoton da ke nuna ta'asar da aka aikata akan fararen hula ciki har da kashe mutane akalla 20 a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/17WV9
Hoto: dapd

Kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadarai da kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da sojojin Mali suka yi a lokacin kubutar da arewacin kasar daga hannun masu kaifin kishin addini. kana ta nemi a gudanar da bincike game da samame da ya kashe fararen hula 11 wanda sojojin Faransa suka yi kai ta sama a ranar da suka fara yaki a Mali. Ita dai kungiyar da ke da cibiyar ta a birnin London na Birtaniya ta wallafa rahoton ne bayan ta shafe kwanaki goma ta na jin ta baki wadanda walau suka shaidar da ta'asar, ko kuma suka rasa wani dan uwa a birane hudu na Mali.

Ita kuwa ana ta bangaren kungiyar Human Right Watch ta zargi masu kaifin kishin addini da kashe sojojin Mali bakwai a birnin Konno ciki har da wadanda suka samu rauni. Kana ta zarge su da amfani da yara a matsayin dakarun yaki. Kungiyoyin biyu da suka himmatu wajen kare hakkokin bani Adama sun nemi hukumomin Mali suka kafa kwamitin bincike domin gaskiya ta yi halin ta game da cin zarafi fararen hula a lokacin fattatakar masu kaifin kishin addini daga arewacin kasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman