Zargin juyin mulki a jamhuriyyar Bini | Labarai | DW | 04.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zargin juyin mulki a jamhuriyyar Bini

Bayan zargin hallaka shugaba Yayi Boni da guba, hukumomi sun sake zargin na hannun damansa da yunkurin juyin mulki.

Hukumomi a jamhuriyyar Bini sun fadi - a wannan Litinin cewar hamshakin dan kasuwar audugar nan, wanda ake nema ruwa a jallo, da yunkurin yin anfani da guba domin kissan shugaba Thomas yayi Boni na kasar, ana kuma dangantashi da yunkurin juyin mulkin daya yi sanadiyyar tsare wasu mutane biyu a kasar. Patrice Talon, da ke zama tsohon na hannun daman shugaba Yayi, ana zarginsa da kasancewa cikin wadanda ke da hannu wajen yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Yayi a wannan Lahadin.

A dai watan Oktoba ne hukumomin kasar ta Bini suka zarge shi da laifin yumkurin da bai yi nasara ba na musayar wani maganin cutar zuciyar da shugaban ke yin anfani da shi da guba domin hallaka shugaban.

Sai dai kuma 'yan adawa a kasar na dasa ayar tambaya dangane da ko hukumomin na yin anfani da wadannan zarge zargen ne domin shafawa masu hamayya da shi kashin kaza. Tuni kuma babban mai gabatar da kara a kasar Justin Gbenameto ya ce suna kan hanyar bayar da sammaci na kasa da kasa domin cafke Talon din.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe