1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin gallazawa fararen hula a Mali

January 30, 2013

Dakarun Faransa sun kwace iko da babban filin jirgin saman birnin Kidal daga hannun 'yan tawayen Mali, yayin da ake zargin sojin gwamnati da cin zarafin jama'a.

https://p.dw.com/p/17U9r
Malian soldiers wait at a checkpoint near Sevare on January 27, 2013. French-led troops were advancing on Mali's fabled desert city of Timbuktu on Sunday after capturing a string of other towns in their offensive against Islamist militant groups in the north of the country. Meanwhile, African leaders meeting in the Ethiopian capital were discussing scaling up the number of African troops to join the offensive, after the African Union's outgoing chief admitted the body had not done enough to help Mali. AFP PHOTO / FRED DUFOUR (Photo credit should read FRED DUFOUR/AFP/Getty Images)
Hoto: Fred Dufour/AFP/Getty Images

Kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na kasa da kasa sun zargi dakarun Mali da yin ramuwar gayya akan wadanda suke ganin ko dai mambobin kungiyoyin masu kishin addini ne ko kuma magoya bayansu ne a biranen Timbuktu da Gao da kuma sauran yankunan da suka kwace iko da su a yanzu.

Baya ga ramuwar gayyar, rahotanni na nuna cewar wasu Larabawa 'yan asalin Mauritaniya da Aljeriya sun fuskanci wawushe dukiyoyinsu a wuraren sana'oin su, da ma matsugunansu musamman a biranen Gao da Timbuktu bisa zargin suna boye makamai ko kuma na'urorin sadarwa da ke taimakawa fafutukar da masu kishin addinin ke yi.

Cheikh Doucoure, magajin garin Tele, wanda kuma mamba ne a majalisar wakilan da suka fito daga yankin arewacin Mali, ya ce labarin da suka samu daga Timbuktu, ba mai dadin ji ba ne:

Ya ce " Mun gudanar da wani taro da ya hada daukacin zababbun yankin arewaci. An sanar da mu a can cewa wasu bata gari sun kwashi dukiyoyi a wasu kantuna mallakar larabawa. Wannan ya yi matukar susa mana zukata. saboda haka ne muka tuntubi shugaban majalisar jihar Tombouctou inda muka bukace shi da ya tuntubi hukumomi domin su tura sojojin da za su sa idanu akan kantuna."

French Prime Minister Jean-Marc Ayrault answers a question on January 29, 2013 during a weekly session of questions to the Government at the National Assembly. AFP PHOTO/JACQUES DEMARTHON (Photo credit should read JACQUES DEMARTHON/AFP/Getty Images)
Firayiministan Faransa, Jean-Marc AyraultHoto: Getty Images

Martanin Faransa akan zargin take hakkin bil'Adama a Mali

Tuni dai kasar Faransa ta bukaci tura wata tawagar sanya ido ta kasa da kasa domin tantance zargin take hakkin bil'Adamar da ake yiwa dakarun, da ma wasu al'ummomin yankunan da a yanzu 'yan tawayen suka tsere daga wuraren.

Akan hakane firayiministan Faransa Faransa Jean-Marc Ayrault ya ce ko da shike ba a kai ga samun hujjojin da ke tabbatar da zargin da ake yi ba, amma akwai bukatar samar da tawagar da za ta tabbatar da cewar ana mutunta hakkin bil'Adama a kasar ta Mali. Yana mai cewar Faransa ta umarci dakarunta da ke Mali su bi lamura sannu a hankali wajen mayar da martani ga rikicin, wanda a yanzu ya jefa ba wai kawai al'ummomin kasar cikin mawuyacin hali ba, a'a harma da ita kanta gwamnati da kuma masu sana'oin da ke fuskantar muzgunawar.

abinda kuma Sebana Maiga, mataimakin magajin garin Gao, garin da a yanzu ya kubcewa 'ya tawayen ya ce kamata yayi a manta da baya domin samun kyakkyawar rayuwa a nan gaba:

Ya ce " Ya zama dole mu rayu tare. Daya bangaren ba zai iya rayuwa ba tare da gudunmawar daya bangaren ba. Kun ga halin da gari ke ciki musamman ma a fannin tattalin arziki. Da ma albashin da ma'aikatan gwamnati ke karba ne ke raya birnin Gao. Amma a halin yanzu an mayar da su kudancin kasa. Kananan ma'aikata ne kawai suka rage a nan. Wannan ne ummal Aba'isan koma-bayan tattalin arziki da muke fuskanta."

Human Rights Watch Logo

Tushen zargin take hakkin bil'Adama a Mali

Idan za'a iya tunawa dai tun a ranar 19 ga watan Janairun nanne, kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Human Rights Watch ta bayyana damuwarta game da zargin cewar dakarun Mali na cin zarafin Larabawa da Abzinawan da ake ganin magoya bayan masu kishin addinin ne a yankin arewacin kasar ta Mali.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani